Kananan yara ba su da makwanci a sansanin Calais da ke Faransa

'Yan gudun hijira

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan gudun hijirar sun kwana a wajen cibiyoyin da ake tantancesu

Masu aikin agaji sun ce kusan yara 100 ba su da makwanci mai kyau, amma kuma shugaban gwamantin lardin ya ce yara 68 ne.

Fabienne Buccio ya ce wasu daga cikin mutanen da suka saura a sansanin ba daga nan suke ba tun asali.

Gwamnatin Faransa ta ce an kwashe kusan mutum 5,600 zuwa cibiyoyin da za a ba su kulawa tun ranar Litinin.

Wadanda aka kwashe sun hada da yara 1,500 wadanda ke zauna a cikin baca a sansanin kuma ba tare da kowa ba.

Masu fafutuka sun ce a yanzu haka wurin ya cika.

Sansanin dai ya zama wata babbar alama ta rikicin 'yan gudun hijira a Turai inda mutanen da ke zaune a cikinsa ke so su isa Ingila.

Masu aikin rusa sansanin dai na ci gaba da kwashe ragowar tantuna daga yankin, wanda ya lalace sakamako wuta da 'yan gudun hijirar da ke barin wurin suka cinna masa.