Japan ta tsare wata 'yar Najeriya da ke neman mafaka

Sojojin Japan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kebe Elizabeth Aruoriwo Obueza makwanni biyu a wani dan karamin dakin gidan yari, har kusan wa'adin sa'o'i 22 a kowacce rana.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Japan sun yi kira da a saki wata mata 'yar Najeriya da ake rike da ita a kebabben dakin yari, bayan da kasar ta ki amincewa da bukatarta ta neman mafaka.

Makwanni biyu kenan ana tsare da Elizabeth Aruoriwo Obueza, bayan da hukumomi suka yi watsi da zargin da ta yi cewa tana bukatar mafaka a Japan ne saboda tsangwamar da take fuskanta a gida, saboda addininta.

Tun lokacin dai aka kebe ta a wani dan karamin dakin gidan yari, har kusan wa'adin sa'o'i 22 a kowacce rana.

Japan dai ta yi watsi da kashi 99 cikin dari na duk wasu bukatun neman mafaka a kasar, inda ta dauki nauyin 'yan gudun hijira 27 kawai.

Lauyan Misis Obueza ya shaida wa BBC cewa hukumomin sun sanya ta a gaba ne saboda ta shigar da koken da ya bukaci gwamnatin Japan din da ta gyara yadda take kula da masu neman mafaka a kasar.