Sudan ta Kudu: Kai Tap ya shafe kwanaki a boye cikin ruwa

Kai Tap dan gudun hijirar Sudan Ta Kudu
Bayanan hoto,

Kai Tap ya shaida wa BBC cewa: "Muna gudu mu yi nutso cikin ruwa domin tsere wa mayakan, kawunan mu kadai ke waje"

Kai Tap, mai shekara 11 ya zauna shi kadai yana muzurai, yayin da ya ke kallon sauran yara suna wake-wake da wasanni a makarantar Eden, wacce ke karkashin kariyar jami'an tsaron na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.

Bai dade da isa sansanin 'yan gudun hijrar da ke garin Bentiu ba, da ke arewacin kasar, bayan ya yi tafiyar kilomita 129 shi kadai cikin kwana hudu daga Leer, inda fada ya kaure a 'yan kwanakin baya.

Kai Tap ya ce fadace-fadacen ne suka ingiza shi ya tsere daga sansaninsu ya bar 'yanuwansa a can.

Ya ce, "Da dare ya yi sai su zo su yi ta harbin mu, mu kuma sai duk mu watse."

"Muna gudu mu yi nutso a cikin ruwa domin boyewa maharban," in ji Kai.

Kai Tap ya ce ba zai iya tuna wa ko kwanaki nawa ya yi a cikin ruwan ba.

An sace garken shanun iyayensa, aka kuma kashe dan'uwansa da ke kula da shanun, tare da rusa gidansu.

Duk da ya samu mafaka, yana cikin damuwa game da halin da 'yanuwansa ke ciki.

Bayanan hoto,

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce miliyoyin yara ne ke fuskantar matsananciyar yunwa

Kai ya kara da cewa, "Ban san halin da suke ciki ba, ko suna raye ko sun mutu, saboda har yanzu ana cigaba da fada."

"Hankali na ya rabu biyu, ina so in shiga makaranta, amma kuma ina so in koma in dauko iyayena."

Hauhawar farashin kayayyaki ya haura kashi 700%

Tsohon shugaban Botswana Festus Mogae, wanda ke jagorantar hukumar da ke sa ido kan yarjejniyar zaman lafiyar 2015, ya ce rikicin da ke faruwa zai iya tayar da kurar wani rikicin da ba za a iya kwantarwa ba.

Akwai rahotannin da ke cewa ana fada a Yei, garin da ke kudu maso gabashi, da Leer da ke arewaci da kuma Nasir da shi ma ke kudu maso gabashin kasar.

Bayanan hoto,

Masu aikin agaji na dogara ne da jiragen sama domin kai kayan tallafi

A sakamakon tabarbarewar yanayin, ba a iya daukar kaya ta hanya.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kara rincabewar rikicin na nufin cewa dole su kara kai kaya da ma'aikata da jami'an tsaro.

"Rashin abinci mai gina jiki a arewacin Bhr al-Ghazal ya karu da ninki uku , don haka dole mu kasance da ninki uku na kayan agaji don tinkarar bukatun yara", Inji Mahimbo Mdoe, wakilin Unicef a kasar.

Ya ce yanayin yayi kamari inda yara kusan miliyan shida ne abun ya shafa.

Ya yi gargadin cewa muddun abubuwa ba su sauya ba, yanayin zai iya ta'azzara ga fararen hula, musamman mata da yara, kuma zai kasance abu mai wuya ga ma'aikatan bayar da agaji su kai gare su.

Bayanan hoto,

Daruruwan fararen hula ke neman mafaka a sansanonin da ke da kariyar jami'an Majalisar Dinkin Duniya

A cikin watan Agusta, kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, ya zartas da wani kuduri na kirkirar rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen yankin (RPF).

Ikon da aka ba ta ya hada da tabbatar da tsaron Juba a matsayin wani wurin da fadan bai shafa ba a gwagwarmayar neman iko tsakanin Shugaba Salva Kiir da kuma Mataimakinsa da aka kora, Riek Machar.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta amince da a tura rundunar, to amma tare da sharuda.

Kakakin Shugaba Kiir, Ateny Wek ya ce gwamnati za ta tantance "daga inda dakarun suka fito da kuma inda rundunar kariyar za ta kasance".

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An nada Riek Machar ( daga hannun hagu) a matsayin mataimakin shugaban kasar Salva Kiir(hannun dama) a wata yarjejeniyar zaman lafiya

Idan har aka yi nasarar cimma yarjejeniyar, to zai dauki watannin da dama kafin ta isa Sudan Ta Kudu.

Yanzu dai Kai Tap na da damar zuwa makaranta, amma sakon sa ga shugabannin kasar tasa da ke cikin rudani shi ne, su tsayar da fadan hakan nan.