Za a kara wa ma'aikata albashi a Venezuela

Nicolas Maduro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Venezuela na fuskantar karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, ya yi tayin karin kashi 40 cikin 100 na albashi mafi kankanta ga ma'aikata, wannan shi ne karo na hudu da ake yin haka a cikin shekarar nan.

Wannan na zuwa ne kwana guda da dubban masu zanga-zanga suka cika titunan kasar, dan nuna adawa da gwamnati.

Venezuela da ta kasance cikin kasashe masu arzikin mai a duniya, na fama da karancin abinci, da kuma hauhawar farashin kayayyaki.

Al'umar kasar sun yi bore ne, bayan an soke shirin kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a a kokarin da ake yi na tsige shugaba Maduro daga mukamin sa.

A gobe juma'a ne kuma 'yan adawa sukai kiran a gudanar da yajin aiki, tare da fitowa tituna dan nuna adawa ga gwamnati