Duterte: 'An min wahayi na daina kalaman batanci'

Rodrigo Duterte

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kalaman Mista Duterte na janyo cece-kuce

Shugaba Rodrigo Duterte na Philippines ya yi alkawarin zai daina yin kalamai masu janyo cece-kuce, bayan da ya yi ikirarin cewa an yi masa wahayi ya daina yin hakan.

Mista Duterte wanda a baya ya kira Fafaroma Francis da shugaba Obama 'ya'yan karuwai, ya ce wannan mataki ya zo masa ne a lokacin da yake cikin jirgi kan hanyar komawa gida bayan ziyarar aiki da ya kai kasar Japan.

Ya kara da cewa a lokacin da kusan dukkan mutanen da ke jirgin ke sheka bacci har da salabba, sai ya ji wa ta murya ta na gargadin sa da cewa '' idan ba ka daina kalaman da ka ke yi marasa kyau ba, sai na kifar da jirgin nan''.

Ya tabbatarwa jama'a a garinsu da ke Davao, alkawarin da ya yi tsakanin sa da Ubangiji, to tamkar da al'umar Philippines ne.

Kalaman da ya yi na baya-bayan nan kan hanyarsa ta zuwa Japan, sun bai wa kowa mamaki inda ya ce baya bukatar sojojin kasar waje, duk da cewa a baya yayi alkawari da Amurka dakarun ta za su yi amfani da sansanin sojin kasar guda buyar.