Antarctic: An cimma yarjejeniyar kare halittun ruwa

Nau'in agwagwa Penguins

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akwai tarin halittun ruwa a cikin tekun Antaktika

An cimma wata yarjejeniya da aka dauki shekaru masu yawa ana tattaunawa, da za ta samar da yanki mafi girma na duniya da zai kare halittun ruwa a tekun Antaktika.

Kasashen Amurka da New Zealand ne za su kula da ikon yankin sama da murabba'in kilomita miliyan daya da rabi.

Yankin da ya kasance mazaunin nau'in agwagwar ruwa da ake kira Penguins a turance.

Wakilin BBC yace an shafe sama da shekaru goma ana gadin yankin da ke Antaktika, babu wata kulawa da ake baiwa tekun da ya hada kasashe da dama.

Tekun mai kankara shi ne mazaunin kashi uku na agwagwar ruwan ko Penguean da ake da ita da kuma tarin halittun ruwa.

Rasha dai ta dade ta na son ganin ba a cimma yarjejeniyar ba, sai dai ministan harkokin wajen New Zealand Murray McCully yace kasashe 24 da suka tattaunawar isun sa tabbatar da tsare halittun tekun.