Kenya ta dauki matakin hana satar amsa

Asalin hoton, Getty Images
A makon gobe ne ake sa ran za a soma babbar jarrabawar kasar
Hukumomin ilimi na kasar Kenya sun kaddamar da wasu sababbin dokoki da zummar hana dalibai satar amsa a lokutan jarrabawa.
Satar amsa dai ta yi kamari a kasar ta Kenya a shekarun baya bayan nan.
Wata sanar da hukumar ilimin kasar ta fitar ta ce za a daina barin dalibai suna yin amfani da raskwana da alluna a lokutan jarrabawa.
Kazalika an haramta shiga dakin jarrabawa da wayar salula.
Hukumomin sun kara da cewa za a sanya ido kan shugabannin makarantu da malamai domin tabbatar da cewa ba sa taimakawa dalibai wajen satar amsa.
A farkon wannan shekarar dai an rusa majalisar da take lura da jarrabawar kasar bayan an gano wata cuwa-cuwa kan yadda aka shirya jarrabawar sakandare ta shekarar 2015, lamarin da ya sa aka soke sakamon jarrabawa na dalibai 5,000.
A makon gobe ne ake sa ran za a soma babbar jarrabawar kasar.