FA tana tuhumar David Moyes

Maki biyu kacal Sunderland ta samu a karkashin jagorancin Moyes

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Maki biyu kacal Sunderland ta samu a karkashin jagorancin Moyes

Hukumar kwallon kafar Ingila tana tuhumar kocin Sunderland David Moyes da zargin aikata ba daidai ba bayan an kore shi daga filin wasa ranar Laraba.

FA ta ce ana zargin "Moyes da furta kalaman batanci ga alkalan wasa."

Lamarin ya faru ne a minti na 90 na wasan bayan alkalin wasa Chris Kavanagh ya ki sauraron karar da aka kai masa bayan an yi wa dan wasan kungiyar Victor Anichebe laifi a da'irar mai tsaron raga.

Sunderland ta sha kashi a wasan da ci 1-0.

Moyes, wanda aka nada shi a matsayin kocin Sunderland a watan Yuli kuma maki biyu kawai suka samu a wasa tara da suka buga.

Yanzu dai Moyes yana da wa'adin zuwa ranar Talata domin ya daukaka kara.