Babu 'yan daba a kwallon kafar Ingila -Wenger

Wenger bai damu da wasan da za su yi da West Ham ranar uku ga watan Disamba ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wenger bai damu da wasan da za su yi da West Ham ranar uku ga watan Disamba ba

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai yarda akwai matsalar 'yan daba a kwallon kafar Ingila ba, yana mai yin kira da a dawo da wurin da ake barin 'yan kallo su zauna domin kada a tayar da yamutsi a filin wasa.

Dandazon 'yan kallo ya kawo cikas a wasan da West Ham ta yi da Chelsea ranar Laraba.

Wenger, mai shekara 67, ya yi mamakin yamutsin da aka tayar, yana mai cewa "ba mu saba ganin irin hakan ba a Ingila."

Ya kara da cewa "ba zai yiwu ka yi kudin-goro ba don kawai mutum 200 sun tayar da hargitsi."

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta goyo bayan dawo da wurin da ake barin 'yan kallo su zauna domin kada a tayar da yamutsi a filin wasa a shekarar 2014.