Buhari zai kashe $10bn a Naija Delta

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanonin da ke hakar mai sun lalata muhalli
Gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari za ta kashe $10bn a yankin Naija Delta da zummar kawo karshen hare-haren masu tayar da kayar-baya.
Minista a ma'aikatar man fetur Emmanuel Ibe Kachikwu, wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa za a yi amfani da kudin ne domin gina hanyoyin mota da na jirgin kasa da makamantansu.
Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin da masu tayar da kayar-baya na yankin ke ci gaba da fasa bututan mai, lamarin da ya sa kasar ta yi asarar biliyoyin naira.
Mr Kachikwu ya ce Shugaba Buhari zai gana da masu tayar da kayar-bayan da masu rike da sarautun gargajiya na yankin a makon gobe.
Su dai masu tayar da kayar-bayan suna so ne gwamnati ta kashe kudade da dama a yankin domin rage radadin talaucin da ke addabarsu.
Masu sharhi dai na dora laifin talaucin da yankin ke fama da shi a kan 'yan siyasar yankin, wadanda suka gaza inganta rayuwar talakawa.