Kocin Everton Koeman na zawarcin Wayne Rooney

Rooney ba shi da makoma a United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rooney ba shi da makoma a United

Kocin Everton Ronald Koeman ya ce zai ji dadi sosai idan kyaftin din Manchester United Wayne Rooney ya koma kungiyar.

Jaridu da dama sun yi hasashen cewa Rooney, mai shekara 31, ba shi da makoma a United bayan da kocin kungiyar Jose Mourinho ya ki sanya shi a wasa.

Sai dai Koeman ya ce, Rooney "Dan wasa ne mai kwazo kuma har yanzu yana haskakawa."

Amma Mourinho ya jaddada cewa Rooney - wanda a yanzu kwallaye uku ne kadai suka hana shi zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a kungiyar - yana cikin tsare-tsarensa.

Koeman ya kara da cewa: "Ban san halin da yake ciki ba, kuma bana son yin katsalandan. Amma idan Rooney ya dawo Everton za mu ji dadi."

Rooney ya koma United daga Everton a kan £27m a shekarar 2004, kuma ya zura kwallaye 246 a wasanni 532 da ya buga.