Mutane 9 ne suka mutu a harin Maiduguri

Sojoji sun sha alwashin murkushe Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojoji sun sha alwashin murkushe Boko Haram

A Najeriya, mutane tara ne aka tabbatar da sun mutu lokacin da wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da harin bama-bamai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rahotanni sun ce wasu 'yan kunar bakin wake ne suka tayar da bama bamai guda biyu, daya a kusa da kofar shiga sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, sannan dayan a wani gidan man NNPC.

Hukumar bayar da agajin gaggawa a kasar, NEMA, ta ce wasu mutane 24 sun samu raunuka.

Birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram, kodayake yanzu ba safai ake kai masa hare-hare ba.

Dakarun sojin Najeriya na cewa suna bakin kokarinsu na kawar da kungiyar ta Boko Haram, suna masu kira ga mutane cewa su rika kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba.