BBC ta karrama matan da suka lashe gasar Hikayata

Aisha Sabitu ta yi kukan murna
Bayanan hoto,

Aisha Sabitu ta yi kukan murna

Gidan rediyon BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai.

An gudanar da gagarumin bikin karrawar ne a otal din Sheraton da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Aisha Muhammad Sabitu ta zama gwarzuwar gasar, inda aka ba ta lambar yabo da kuma $500.

Aisha, wacce ta fito daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labarinta ne mai suna "Sansanin 'Yan Gudun Hijira".

Labarin nata ya yi tsokaci ne kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suka samu kansu a wani sansani da ke jihar Adamawa.

Bayanan hoto,

Amina Gambo ta ce za ta ci gaba da rubuta kagaggun labarai

Amina Hassan Abdulsalam ita ce ta zo ta biyu a gasar, inda ta rubuta labari mai suna "Sai Yaushe?", yayin da Amina Gambo ta zo ta uku da labarinta mai taken "In Da Rai".

An zabi labaran ne bayan fafatawar da matan da suka shiga gasar suka yi, kana alkalai kan gasar suka tantance labarai uku da suka dace da ka'idojin da aka shimfida.

Da take karbar lambar yabonta, Aisha Sabitu ta barke da kukan murna, kuma ta yi godiya ga Sashen Hausa na BBC bisa wannan gasa da ya kirkiro ta mata zalla.

Bayanan hoto,

Amina Hassan Abdussalam ce ta zo ta biyu

Wannan ne karo na farko da Sashen Hausa na BBC ya sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla.

Editan riko na BBC Hausa, Jimeh Saleh, ya ce: "Mun gamsu da irin yadda aka nuna sha'awar shiga gasar da kuma irin labaran da aka turo, muna kuma farin ciki ganin cewa mun bai wa mata damar fadar labaransu. Fatanmu shi ne mata iyayenmu sun rungumi harkar rubutu na kagaggun labarai."