Na fi so Ronaldo ya lashe Ballon d'Or —Zidane

Ronaldo bai zura kwallaye sosai a bana ba
Bayanan hoto,

Ronaldo bai zura kwallaye sosai a bana ba

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce Cristiano Ronaldo ne ya fi cancanta ya zama zakaran kwallom kafar duniya duk da cewa bai zura kwallaye da yawa a bana ba.

Zidane ya kara da cewa Ronaldo yana gaban Lionel Messi wajen dacewa da lashe gasar ta Ballon d'Or.

Ronaldo, mai shekara 31, na cikin 'yan wasan da aka sanya sunayensu domin fafatawa wajen lashe gasar bayan ya jagoranci Portugal ta dauki kofin Euro 2016.

Sai dai ya yi ta samun koma-baya a kakar wasa ta bana, inda ya zura kwallaye hudu kacal a wasanni tara da ya buga.

Kocin na Real Madrid, Zidane, ya ce Ronaldo ne "mutumin da ya fi dacewa da lashe gasar ba wai don rawar da ya taka shi kadai ba, sai domin tallafa takwarorinsa da yake yi domin su zura kwallo."

Zidane ya ce Ronaldo ya san cewa nasarar da yake tamu ta faru ne sakamakon aiki tukuru da yake yi da kuma taimakwa 'yan wasan da ke tare da shi.

Ronaldo, wanda sau uku yana lashe Ballon d'Or, da kuma mai rike da kambun gasar Messi na cikin 'yan wasa 30 da aka ware sunayensu domin lashe gasar ta bana.

Dan wasan ya zura kwallaye 368 a fafatawa 357 da ya yi tun lokacin da ya koma Real Madrid daga Manchester United a shekarar 2009.