Wani jirgi ya kama da wuta a Amurka

Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Miami

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Miami

Wani jirgin Amurka ya kama da wuta a filin jiragen sama na O'Hare da ke Chicago lokacin da yake kokarin tashi.

Jirgin, samfurin Boeing 767 wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Miami, ya gamu da matsalar inji, a cewar jami'an da suka gudanar da bincike a kansa.

Matukin jirgin ya fasa tashi kuma nan take aka kwashe mutanen da ke cikinsa a daidai lokacin da wani hayaki ke fitowa daga cikinsa.

Hukumar kwana-kwana ta ce mutum ashirin ne suka samu raunuka.

Ta kara da cewa kawai fasinjoji 161 da kuma matuka jirgin tara a cikin jirgin lokacin da lamarin ya faru.