Zaben Ondo: An yi zanga-zanga a Akure

Masu zanga-zanga da jami'an tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matasa a Najeriya sun sha fitowa zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da wanda zai jagorancesu

Matasa sun fita kan tituna inda suka yi zanga-zanga a birnin Akure na jihar Ondo, a Nigeria, domin nuna rashin amince wa da dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar.

A ranar Alhamis ne hukumar zabe ta INEC ta sanar da Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar jam'iyyar, wacce ke mulkin jihar.

Shi dai Mista Ibrahim yana bangaren PDP ne da ke biyayya ga Sanata Ali Modu Sheriff.

Hakan ba karamin koma-baya ba ne ga gwamnan jihar Olusegun Mimiko, da kuma dan takar da ya tsayar Eyitayo Jegedea, wadanda ke biyayya ga bangaren Sanata Ahmed Makarfi.

A rana 26 ga wantan Nuwamba ne za a gudanar da zaben.

Masu zanga zangar suna goyon bayan Eyitayo Jegede, wanda ke cikin wani bangaren jam'iyyar Makarfi. Ibrahim ya yi takara a karkashi bangaren Ali Modu sheriff.

Jerin sunayen 'yan takarar gwamna da hukumar INEC ta wallafa a ranar Alhamis, shi ne jerin sunaye na karshe na 'yan takarar gwamna kuma sun hada da 'yan takara 27.

Yayinda da ake kone-konen tayoyi da kuma toshe hanyoyi a wasu wurare na birnin, kwamandan 'yan sanda ya bayar da tabbaci ga mazauna Akure cewa ba sa tare da wani hadari.

Mai Magana da yawun 'yan sandar jihar, ASP Femi Joseph, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya ce NAN cewa, 'yan sanda sun jaddada anniyarsu ta kare lafiya da dukiyoyin mutanen jihar.