Mataimakin Trump, Mike Pence ya tsallake rijiya da baya

Jirgin da ya kauce hanya a filin saukar jirgin LaGuardia
Bayanan hoto,

Jirgin da ke dauke da Mista Pence ya samu tsayawa ne a kan ciyayi

Mataimakin dan takarar shugaban kasar Amurka Mike Pence ya tsallake rijiya da baya, bayan da jirgin da yake ciki ya kauce hanayarsa a yayin da yake sauka a filin saukar jiragen birnin New York.

Gwamnan na jihar Indiyana ya shaida wa manema labarai cewa yana cikin koshin lafiya, duk da tangardar da aka samu a filin saukar jiragen LaGuardia.

Babu labarin ko wasu sun samu rauni a lamarin.

Matukin jirgin ya hanzarta danna birki domin tsayar da jirgin, ta yadda har fasinjojin suka iya shakar kurar da tayoyin jirgin ke yi.

Ta bayan jirgin aka fitar da Mista Pence tare da sauran fasinjojin da ke cikin jirgin su 30.

Lamarin ya afku ne a yayin da Mista Pence ke dawowa daga wani taron kamfe a Forte Fort Dodge da ke jihar Iowa.

An dai rufe filin saukar jiragen saman LaGuardia bayan afkuwar lamarin.