Ana binciken manyan jami'ai a Kenya kan rashawa

Tutar kasar Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyata, ya bayyana takaicinsa game da yadda, a cewarsa, wasu bata gari ke yiwa gwamnatinsa gwamnatin zagon kasa

Hukumomi a Kenya na bincike kan zargin almundahana da kudi dala miliyan 50 da ake wa wasu manyan jami'an gwamnati a ma'aikatar kiwon lafiya.

An bayar da kudaden ne domin gudanar da wani shiri da gwamnati ke son kaddamarwa, wanda zai samar wa masu juna biyu kulawa kyauta.

Sakataren ma'aikatar kiwon lafiyar Mista Cleopa Mailu, ya nuna bacin ransa game da yadda rahoton badakalar ya fito a jaridu, tun kafin a kammala binciken.

An wallafa labarin binciken da ake gudanarwar a ma'aikatar a cikin wata jaridar kasar, Business Daily, abin da ya janyo cece-ku-ce tsakanin shugabannin jam'iyyun adawa, inda suka yi ta kira da a sallami duk jami'an da ke da hannu cikin cuwa-cuwar.

Hukumar binciken manyan laifuka, watau Directorate of criminal Investigation, da Hukumar da'a da yaki da rashawar kasar, watau The Ethics and Anti-corruption Commission, da kuma hukumar bincike ta kasar, duka suka dukufa suna bincika lamarin.

Jaridar Business Daily ta wallafa ne ranar Talata a wani rahoto na musamman, cewa ana zargin sun karkatar da dala miliyan 50 din da aka ware domin duba lafiyar masu juna biyun ne, ta kamfanonin da suka mallaka da kuma kin sayen wasu kayayyaki da ya kamata su saya ba.

Makwanni biyu kacal da suka wuce ne shugaban Kenya, Uhuru Kenyata, ya bayyana takaicinsa game da yadda, a cewarsa, wasu bata gari a gwamnatinsa ke yiwa gwamnatin zagon kasa, wajen ganin an yaki cin hanci da rashawa.