Sojojin Najeriya sun sako yara 900

Yaran da sojoji suka ceto a hannun Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Garuruwa da dama sun kyamaci yaran saboda suna ganin suna da wata alaka da kungiyar na Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi nasarar sa baki wajen ganin an sako wasu yara 900 daga hannun jami'an tsaro , a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya , a sakamakon wata tattaunawa da suka yi da su.

Wani jami'i a asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, ana tsare ne da yaran a barikin soji, bisa zarginsu da alaka da kungiyar Boko Haram.

A baya dai yaran na zama ne a wasu yankuna da ke karkashin ikon kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci.

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce, akwai garuruwan da suka kyamaci yaran saboda suna kallon su da wata alaka da mayakan na Boko Haram.

Sojojin Najeriyar dai sun kwato yawancin yankunan da ke hannun 'yan kungiyar a yanzu.