Binciken FBI: Na tabbata ina da gaskiya -Clinton

Asalin hoton, Getty Images
Wikileaks sun yi ta kwarmata bayanan sakwannin emails din Misis Clinton kusan a kowace rana
Hillary Clinton ta ce ta yi imanin cewa sabon binciken da hukumar binciken manyan laifukka ta kasar Amurka (FBI) za ta soma kan sakonninta na email ba zai samar da wani sakamako da ya bambanta da na farko ba; wanda ya nuna ba ta da laifi.
'Yar takarar ta jam'iyyar Democrat ta bukaci daraktan hukumar ta FBI da ya bayyana wa Amurkawa sakamakon bincikensa.
Shugaban Hukumar ta bincike ta FBI, ya ce ta soma bincike kan sabbin sakonnin email, da ke da alaka da 'yar takarar shugabancin Amurka Hilary Clinton.
James Comey ya ce, a baya ya fadawa Majalisar Dokokin Amurkan cewa, Hukumar ta FBI ta kamala binciken da ta ke yi, kan sakonnin email din Misis Clinton din na kashin kanta.
Mista Comey ka kuma ce a yanzu hukumar na gudanar da bincike, domin tantance ko sabbin sakonin email din, sun kunshi wasu bayanan sirri.