Kompany zai ci gaba da murza leda a City -Guardiola

Kompany ya buga wa City wasa 33 a shekarar 2014 zuwa 2015

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kompany ya buga wa City wasa 33 a kakar wasa ta shekarar 2014 zuwa 2015

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce Vincent Kompany na da kyakkyawar makoma a kungiyar, amma yana bukatar sadaukawar domin ya rika buga wasa akai-akai bayan raunin da ya ji.

Kompany, wanda ya buga wa City wasa sau 22 a kakar wasan da ta wuce, ya ce ya gaji a lokacin wasan da suka yi da Manchester United ranar Laraba, lamarin da ya sa aka maye gurbinsa da Aleksandar Kolarov.

Guardiola ya ce, kwantaraginsa ba ta tare a kungiyar ba don haka babu inda za shi, yana mai cewa "Ya ji rauni sau da dama. Amma muna kokarin sake ba shi damar buga wa."

Kompany ya dauki kofin Premier sau biyu a City a shekarar 2012 da 2014, amma raunukan da ya rika ji sun hana shi katabus a bana.

Ya buga wa City wasa 33 a shekarar 2014 zuwa 2015, kasa da wasa 37 gabanin hakan.

Kompany ya koma City ne daga Hamburg a watan Agustan shekarar 2008 kuma kwantaraginsa zai kare a shekarar 2019.