Gagarumar girgizar kasa ta abkawa Italiya

Masu ibada a coci-coci sun yi ta kansu a yayin da cocin ke ruftawa

Asalin hoton, @MONKSOFNORCIA

Bayanan hoto,

Masu ibada a coci-coci sun yi ta kansu a yayin da cocin ke ruftawa

Wata gagarumar girgizar kasa ta abkawa tsakiyar kasar Italiya kusa da Norcia, inda ta rusa manya-manyan gine-gine.

Girgizar kasar ta abku ne wata biyu bayan wata babbar girgizar kasa ta abkawa kasar, inda t kashe kusan mutum 300 sannan ta lalata garuruwa da dama.

Girgizar kasar da ta faru ranar Lahadi tana da karfin 6.6, fiye da wacce ta faru a watan Agusta, kuma zurfinta ya kai 1.5km.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan yawan mutanen da ta kashe, sai dai an rika jin kananan girgizar kasa a babban birnin kasar na Rome.

Hukumar kula da yanayi ta Amurka ta ce girgizar kasar ta fi karfi a yankin Perugia da Norcia.