Rahama Sadau ta amsa gayyatar Akon zuwa Amurka

Rahama tare da Akon
Bayanan hoto,

Rahama tare da Akon

Jarumar nan da aka kora daga Kannywood bayan an same ta da laifin rungumar wani mawaki, Rahama Sadau, ta tafi Amurka bisa gayyatar da wasu mawaka suka yi mata.

Wasu hotuna da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram sun nuna ta tare da fitaccen mawakin nan na Amurka, Akon, da wasu masu shirya fina-finan Hollywood.

Akon da takwaransa Jeta Amata sun gayyaci Rahama Sadau zuwa birnin Los Angeles ne domin ta halarci wurin da suke hada sabon fim dinsu.

Bayanan hoto,

Rahama Sadau ta yi suna cikin kankanen lokaci

Akon ya ce ya gayyace ta ne domin "na karfafa mata gwiwa sakamakon korar da aka yi mata daga Kannywood."

Sai dai kafin tafiyar tata, fitaccen Malamin addinin Musulincin nan na Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira a gare ta da kada ta amsa gayyatar.

A wata budaddiyar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, wadda kuma ya bukaci a mika sakonsa ga jarumar, ya ce: "Ke dai Musulma ce kuma mu Musulinci shi ne abin dubawa a gare mu."

Sheikh Daurawa ya kuma bukaci jarumar da ta yi aure domin a cewarsa shi ne "ya fi dacewa da ita".

Ita dai Rahama Sadau ta ce rungumar da ta yi wa Classiq ba laifi ba ne, tana mai cewa "ba zai yiwu na yi aiki ba tare da na taba wani ba."

Bayanan hoto,

Akon ya ce yana son karfafa gwiwar Rahama Sadau

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da take jawo ce-ce-ku-ce ba