Na yi shakku kan 'yan wasana - Guardiola

Sergio Aguero ya haskaka a wasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sergio Aguero ya haskaka a wasan

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya amince cewa ya nuna shakku kan 'yan wasansa ba wai kan tsarinsa na buga wasa ba bayan sun doke West Brom, lamarin da ya sa suka zo karshen wasanni shida basu ci kwallo ba.

City ba ta yi nasara a wasa ba tun ranar 24 ga watan Satumba, sai dai ta doke West Brom da ci 4-0 inda ta hau kan tebirin gasar Premier.

Guardiola ya shaida wa BBC Sport cewa "Sau shida muka yi wasa ba mu ci ba, kuma hakan lokaci ne mai tsawon gaske. Duk lokacin da muka sha kashi sai na yi shakkar 'yan wasana. Haka kuma idan muka dawo daga hutun rabin lokaci bamu ci wasa ba sai na yi shakku kan su."

Guardiola ya kara da cewa bai taba yin shakka kan tsarin wasansa ba, yana mai cewa "sake yin nasara yana da matukar muhimmanci a gare mu."

Sergio Aguero ya zura kwallaye biyu a wasan, yayin da Ilkay Gundogan ya kara kwallaye biyu.