An hana Mourinho zuwa filin wasa

Da farko dai an kori Mourinho ne zuwa wajen 'yan kallo, sai kuma ya koma wajen da jami'ai ke zama

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Da farko dai an kori Mourinho ne zuwa wajen 'yan kallo, sai kuma ya koma wajen da jami'ai ke zama

An kori kocin Manchester United Jose Mourinho zuwa wurin da 'yan kwallo ke zama a wasan da suka tashi 0-0 da Burnley na gasar Premier ranar Asabar.

Mourinho ya fito bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sannan aka raka shi wajen tsayawar 'yan kwallo a Old Trafford a wasan da ya sa United koma ta takwas a tebirin gasar Premier.

Daga nan ne kuma dan kasar ta Portugal mai shekara 53 ya tafi wurin da shugabanni ke zama.

Alkalin wasa Mark Clattenburg ya yi watsi da kiran da United ta yi a ba su bugun fenareti.

Wani mai sharhi kan wasanni Danny Murphy ya bayyana cewa kashin da aka rika bai wa United a 'yan kwanakin nan ne ya gigita Mourinho.

Mourinho bai yi magana da 'yan jarida ba bayan wasan, wanda United ta mamaye,inda ta yi yunkurin cin kwallo sau 37.