An kori ma'aikata 10,000 a Turkiyya

Fethullah Gulen ya musanta kitsa juyin mulki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fethullah Gulen ya musanta kitsa juyin mulki

Fethullah Gulen ya musanta kitsa juyin mulki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fethullah Gulen ya musanta kitsa juyin mulki

Hukumomi a Turkiyya sun kori ma'aikata sama da 10,000 wadanda ke da alaka da fitaccen malamin nan da ake zargi da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba.

An yi amfani da wata dokar soja ta gaggawa wajen korar ma'aikatan da suka hada da likitoci da nas-nas da kuma malaman makaranta.

An kuma umarci gidajen watsa labarai 15 su daina aiki.

Babu cikakken bayani kan ko mutanen da aka kora na cikin dubban mutanen da aka dakatar daga aiki, wadanda ake zargi suna da dangantaka da Fethullah Gulen, wanda ke da zama a Amurka.

Mr Fethullah Gulen ya musanta cewa shi ne ya kitsa juyin mulkin, kuma Amurka ta ki amincewa da kiran da Turkiyya ta yi mata domin ta mika mata shi.