Kar ICC ta damu don wasu kasashe sun fice—Bensouda

Mai shigar da kara ta kotun ICC, Fatou Bensouda
Babbar mai shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC, Fatou Bensouda ta ce ka da kotun ta damu don kasashe uku na Afirka sun yanke shawarar ficewa daga cikinta.
A watannan watan ne Burundi da Afirka ta Kudu da kuma Gambia suka ce za su fice daga kotun ta ICC dake da shedkwata a birnin Hague.
Kasashen sun zargi kotun da nuna son kai, domin kusan dukkan shari'o'in da ta gudanar a kan kasashen Afirka ne.
Ms Bensouda ta shaidawa wata jaridar Holland, NRC cewa duk da cewa matakin da kasashen suka dauka bai yi wa kotun dadi ba, amma duk da haka za ta ci gaba da gudanar da shari'a akan manyan laifukan da aka aikata a kasashen Afirkan.
Ta yi kira ga Tarayyar Afirka da ta ci gaba da ba kotun ta ICC hadin kai.