An kashe mutane 25 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

UN peacekeepers

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun ce suna fafutukar dakile fadace-fadace da ke ci gaba da yaduwa a kasar.

Mutane ashirin da biyar ne aka kashe a cikin kwanaki biyun da suka gabata.

Kungiyoyin 'yan bindiga na Musulmi da Kirista sun yi arangama a garin Bambari, inda aka kuma kai hare-hare kan 'yan sanda da kuma dakarun Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu rahotanni sun ce wasu 'yan siyasa na ingiza kungiyoyin daukan makamai don kai hare-hare.

Wasu fadace-fadacen suna da nasaba ne da zirga-zirgar dabbobi.

Fiye da shekaru uku kenan da fara fadace-fadacen a Jamhoriyar Tsakiyar Afirkan, lokacin da 'yan tawaye, akasarinsu, Musulmai suka hambarar da shugaban kasar.