Lugudan wuta ta sama ya halaka fararen hula 17 a Yemen

Asalin hoton, EPA
Fararen hula da dama ne aka kashe a lugudan wuta ta sama a Yemen
Rahotanni daga Yemen sun ce an kashe akalla fararen hula goma sha bakwai a lugudan wuta ta sama da dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta suka yi a wani gari kusa da birnin Taez.
Rahotannin sun ce akasarin wadanda suka mutun matane da yara, kuma sun mutu ne lokacin da bama-bamai suka fada kan gidajensu bisa kuskure.
Birnin Taez, ya kasance wani mashahurin filin daga da ake gwabza fada tsakanin 'yan tawayen Houthi da dakaru masu biyayya ga shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi, wanda Saudiya ke mara wa baya.
An sha sukar dakarun kawancen bisa mutuwar fararen hula da yawa sakamakon lugudan wuta ta sama.