An fara kokarin dawo da hukuncin kisa a Turkiyya

Turkey

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdogan

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya ce gwamnati za ta gabatar da wani kuduri a gaban majalisar dokokin kasar dake neman a dawo da hukuncin kisa a kasar.

Mista Erdogan ya ce zai rattaba hannu akan kudurin idan har majalisar dokokin ta amince da shi.

A shekarar 2004 aka soke dokar hukuncin kisa a kasar, a matsayin wani bangare na yunkurin zama mamba a Tarayyar Turai.

Amma tun bayan yunkurin juyin mulki a kasar, shugaba Erdogan yake kiran a adowa da hukuncin kisan.

Jamus ta yi gargadin cewa, sake bullo da hukuncin kisa a Turkiyan, zai kawo karshen fatan da take da shi na shiga Tarayyar Turan.

Sai dai Mista Erdogan, ya ce bai damu da abin da kasashen Turan za su ce ba game da yunkurin na shi.