Mutane 30 sun mutu a Yemen sakamakon hare-hare ta sama

Mafi yawancin wadanda suka mutu fursunoni ne da ke cikin ginin
Bayanan hoto,

Mafi yawancin wadanda suka mutu fursunoni ne da ke cikin ginin

Wasu hare-hare ta sama da dakarun kawancen da Saudi Arabiya ke jagoranta a Yemen sun hallaka akalla mutane talatin a shalkwatar tsaro da ke yammacin gabar teku ta Hodeida inda 'yan tawayen Houthi ke iko da shi.

Rahotanni sun ce mafi akasarin wadanda suka mutun fursunoni ne wanda ake tsare da su a cikin ginin.

Tunda farko a ranar Asabar, fararen hula goma sha bakwai ne suka rasa rayukansu akasarinsu yara a wasu hare-hare ta sama da dakarun kawancen suka kai a birnin Taez.

Wannan kawance da Saudi Arabiya ke jagoranta na fuskantar suka daga kasashen duniya saboda rasa rayukan fararen hula da dama a sanadiyyar hare-hare ta sama da kawancen ke kaiwa a Yemen.