An kashe fitaccen dan gwagwarmayar siyasa a Libya

Mohammed Bouqaiqis ya mutu ne tare da wasu mutane biyu a harin
Bayanan hoto,

Mohammed Bouqaiqis ya mutu ne tare da wasu mutane biyu a harin

Wani harin bam da aka kai da mota a birnin Benghazi na kasar Libya ya kashe wani fitaccen dan gwagwarmayar siyasa da ke da alaka da wani janar din soji da ya jagoranci yaki da mayakan IS na tsawon shekaru biyu.

Mohammed Bouqaiqis ya mutu ne tare da wasu mutane biyu, yayinda wasu da dama kuma suka jikkata.

Yana gabatar da wani shiri a talbijin, kuma ya nuna goyon baya mai karfi sosai ga yakin da janar din mai suna Khalifa Hifter ke jagoranta da kungiyar IS.

An dai samu cigaba sosai ta fuskar tsaro a Benghazi, amma kuma ana cigaba da fada a wajen birnin.

A ranar jumma'ar da ta gabata ne aka gano gawawwakin wasu maza goma wadanda ba a gano ko suwa ye ba da aka azabtar da su.