Za a yi kuri'ar raba gardama a Ivory Coast kan tsarin mulki

Alassane Ouattara ya ce za a samu cigaba a kasar idan akayi garan bawul a kundun tsarin mulkin kasar
Bayanan hoto,

Alassane Ouattara ya ce za a samu cigaba a kasar idan akayi garan bawul a kundun tsarin mulkin kasar

Ivory Coast zata gudanar da kuri'ar raba gardama a yau akan sabon kundun tsarin mulkin kasar wanda shugaba Alassane Ouattara ya ce zai taimakawa kasar wajen samun cigaba bayan shekarun da aka shafe ana fama da rikici.

Tuni dai jam'iyyun adawar kasar suka yi kiran da a kauracewa wannan yunkuri, suna masu cewa anyi saurin yiwa kundun tsarin mulkin gyare-gyare kuma zai bawa shugaban kasar karfin ikon da ya wuce kima.

Wani babban abu a cikin gyare-gyaren da ake son yi a cikin kundun tsarin mulkin shi ne saukaka ka'idojin zama dan kasa ga 'yan takarar shugaban kasa, wani batu da ya rura wutar yakin basasa har sau biyu a kasar tun shekarar 2002.

Sannnan kuma zai samar da majalisar dattawa a kasar wadda kaso uku na adadinsu shugaban kasa ne zai nada su.