Nigeria: An maido da abincin 'yan gudun hijira da aka sace

Wasu 'yan gudun hijira
Bayanan hoto,

A watan Agusta majalisar dokokin kasar ta ce ta kaddamar wani bincike kan zarge-zargen.

Jami'ai a jihar Borno ta Nigeria sun ce an hannunta musu abincin da gwamnatin tarayyar kasar ta aike wa 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da shi amma sai aka karkata akalar wasu daga cikin motocin da ke dauke da kayan abincin.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Alhaji Ahmed Satomi ya tabbatar wa BBC da cewa sun karbi motoci 79 na kayan abinci daga cikin 113 da gwamnatin tarayyar ta turo; kuma nan ba da dadewa ba za su karbi sauran.

'' Ministan da aka wakilta ya kawo kayan abincin ne ya zo ya kawo wannan abincin da ake tunanin an so a bi wata hanya da shi, amma alhamdulillahi yanzu an gano shi har an hannunta shi ga gwamnatin jihar Borno.'' In ji Alhaji Satomi.

Zargin karkata akalar kayan abincin na 'yan gudun hijra dai ya fusata mutane da dama a kasar tun ma ba 'yan gudun hijiran ba wadanda suka yi zanga-zanga a sansanoni daban-daban.