Clinton: 'Yan majalisar Demokrat sun zargi FBI

Mr. James Comey

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mr. Comey na jin yana da wani nauyi a kansa na gudanar da binciken.

Wasu manyan 'yan majalisar dattawan Amurka na jam'iyyar Demokrat sun rubuta wa hukumar FBI da ma'aikatar shari'ar kasar da wasika suna kira gare su da su yi musu karin bayani game da sakonnin e-mail din suka sa hukumar ta sake sabunta binciken da take yi wa 'yar takararsu.

'Yan majalisar sun ce shawarar da Daraktan hukumar James Comey ya yanke ta sake bude binciken makonni biyu kafin zaben shugaban kasa ya nuna cewa ana amfani da shi ne wajen cimma wata manufar siyasa.

'Yar takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar Jam'iyyar ta Demokrat Hillary Clinton dai ta kira wannan matakin abin da ba a taba gani ba kuma mai sanya damuwa matuka.

Rahotanni dai sun ce jami'an ma'aikatar shari'ar ma sun gargadi Mr. Comey da kada ya dauki wannan matakin.