Sojoji sun dakile yunkurin sabon hari a Maiduguri

Asalin hoton, AFP
Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a Maiduguri
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile wani yunkuri na kai harin kunar bakin wake a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An yi yunkurin kai harin ne kwana daya, bayan wasu 'yan kunar bakin wake da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare a birnin, ciki har da kofar shiga sansanin na Bakassi.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce dakarun rundunar Operation Lafiya Dole dake Maiduguri sun harbe wani dan kunar bakin wake da safiyar Lahadi, yayin da yake kokarin kutsawa cikin sansanin 'yan gudun hijiran na Bakassi.
Kanar Kukasheka ya ce bayan an harbe dan kunar bakin waken, jami'ai tsaro masu kwance bom sun lalata bom din dake jikinsa kafin ya kai ga tashi.
Hare-haren kunar bakin wake na neman dawowa a birnin na Maiduguri, bayan an samu saukin hare-haren na lokaci mai tsawo.