An yi yunkurin kai harin bom a Saudiya

Asalin hoton, AP
Jami'ar tsaro a Saudiya yayin da take sintiri
Saudiya ta ce ta dakile wani yunkuri na kai harin bom a lokacin wani wasan kwallon na kasa-da-kasa a Jedda.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce an shirya kai harin ne ta yin amfani da mota da ke dauke da bom a lokacin wasan tsakanin Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ma'aikatar ta ce ta kuma dakile wani yunkurin na kashe jami'an 'yan sanda, wanda ta ce, wani shugaban kungiyar IS a Syria ne ya bada umurni.
An kama mutane da yawa da ake zargi da yunkurin shirya hare-haren biyu, cikin su kuma har da 'yan kasar ta Saudiya, da wani dan kasar Syria da wasu 'yan Pakistan biyu.