Mutane 10 sun mutu a hare-haren bam a Bagadaza

Iraq

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani wurin da aka kai hari a Iraki

An kai jerein hare-haren bama-bamai a Bagadaza, babban birnin Iraki, yayin da gwamnatin kasar ke ci gaba da yakin fatattakar kungiyar IS daga birnin Mosul.

Wani harin bom na mota ya kashe akalla mutane goma a wata kasuwar kayan miya a gundumar Hurriyah, sannan kuma an kai wasu kare hare-haren a unguwannin 'yan Shi'a a Bagadazan.

Rahotanni sun ce kungiyar ta IS ta na tura karin mayakanta garin Tal Afar dake yammacin Mosul.

Wani jagoran kungiyar 'yan bindiga ya ce yakin kwato birnin na Mosul, abu ne da zai dauki watanni ana yi.