Ana binciken masu satar man ne a yankunan jihohin Legas da Ogun

Najeriya dai na hasarar makudan kudade a kowanne wata a sakamakon satar man fetur
Bayanan hoto,

Najeriya dai na hasarar makudan kudade a kowanne wata a sakamakon satar man fetur

Rundunar sojin ruwan Najeriya, ta ce ta kaddamar da bincike kan wasu jami'anta bisa zarginsu da hannu a satar danyan man fetur.

Ana dai zargin jami'an ne da hada baki da matasan nan masu satar mai a yankunan Areppo da Isawo da kuma Alekpote a jihohin Legas da kuma Ogun.

Rundunar wacce ke kula da sashin Kudu maso Yammacin kasar, ta ce ta kwato jarkoki sama da dubu hamsin daga hannun masu fasa bututun man fetur a yankin.

Rundunar ta ce batagarin na zaune a yankunan ne sama da shekaru 20.

Najeriya dai na asarar makudan kudade a kowanne wata a sakamakon satar man fetur.