Faransa ta janye dakarunta daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Asalin hoton, AFP
An sha yabawa dakarun Sangaris kan nasarar dakile munanan kashe-kashe a yayin yakin basasar kasar
Faransa na shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiyar kasar a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, bayan sun shafe shekaru ukku suna shiga tsakani a rikicin da ya biyo bayan boren da ya yi sanadin tsige Shugaba Francois Bozize.
Janye dakarun Faransan 2,000 na zuwa ne a yayin da aka soma wasu sabbin kashe-kashe a kasar.
Faransa ta ce dakarun Sangaris sun yi nasarar kawo karshen fadace-fadace a Jamhuriyar ta Afirka Ta Tsakiya.
Sai dai dakarun Faransa 350 za su ci gaba da kasancewa a kasar domin tallafawa dakarun Majalisar Dinkin Duniya na Minusca.
Hakan na nufin tunda rundunar Sangaris ta kammala ayyukan ta, yanzu dakarun Minusca ne za a bari da ayyukan tsaro su kadai.
Sai di wakilin BBC kan harkar tsaro a Afirka yace babu kwarin gwiwar cewa za su iya bayar da tsaro ko ma kwantar da tarzomar yadda ya kamata.