Rayuwar 'yan matan Chibok bayan sun kubuta

'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan matan Chibok din da suka koma Amurka a 2014, sun sha fitowa suna bayar da labarin abin da ya faru da su

A jerin wasikunmu daga 'yan jarida a Afirka, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani, ta yi nazari kan rayuwar wasu daga cikin 'yan matan Chibok, da aka ceto daga hannun 'yan Boko Haram a Najeriya.

A wani yunkuri na taimaka wa 'yan matan Chibok 21 din nan da aka ceto kwanan nan daga tsangwama da nuna musu wariyar da ake nuna wa wadanda kungiyar Boko Haram ta sace, wani shugaba a garin Chibok din ya yi kira da a tura su Amurka, domin kammala karatunsu.

To amma kuma akwai wasu matsalolin da matan ke iya fuskanta a kasar waje ma.

Wasu 57 cikin matan da suka iya kubutar da kansu sa'o'i kalilan bayan kungiyar ta sace su daga makarantarsu a watan Afrilun shekarar 2014, a cikin wasu manyan motoci, yanzu haka suna ci gaba da karatunsu na boko a Amurka.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa Adaobi irin murnar da suka yi da jin an sako wasu takwarorin nasu.

Sun kuma ce zai yi kyau su ma a turo so Amurka domin kammala karatunsu, kamar yadda aka yi masu.

Patience Bulus, na cikin wadanda ke karatu yanzu a Amurka, kuma ta ce, "Mai yiwuwa in an kawo su, zai taimaka har su manta da abin da ya faru da su a baya."

Wata daga cikin 'yan matan mai suna Kauna Yaga, ita ma ta ce, "Ba za su ji tsoro ba a nan Amurka, kuma za su manta da abin da ya faru da su."

Amma kuma mantuwa ba ta cikin abubuwan da 'yan matan Chibok ke da ikon yi, kafin 'yan watannin da suka gabata.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan matan Chibok din da suka koma Amurka a 2014, sun sha fitowa suna bayar da labarin abin da ya faru da su

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wata kwararriyar likitar tunanin dan adam mai suna Somiari Demm, wadda ke aikin dawo da su hayyacinsu, su manta da mugun abin da ya faru da su, wadda kuma ke kula da guda 10 daga cikin 'yan matan, ta ce, "kafin watan Mayun shekara 2016, ana musu ba-n-gishiri-in-ba-ka-manda ne, da taimakon da ake ba su.

Suna bayar da labarin abin da ya faru da su ne, sannan kuma a madadin hakan a rika ba su taimako, maimakon a bayar da muhimmanci ga gyara tunaninsu da cigaban iliminsu."

Likitar ta bayyana yadda 'yan jarida suka mayar da hankali a kansu, kullum har kusan shekara biyu, wanda hakan ya katse masu hanzari zuwa makaranta da kuma hazakar su wajen karatu.

A ire-iren wadannan tarukan, ana ingizasu su kara gishiri a bayanan yadda rayuwarsu ta kasance a hannun mayakan Boko Haram din, domin an fi daukar zancen nasu da muhimmanci.

Bayanan nasu sun sha taimaka wa wajen samun tallafi musamman daga coci-coci.

'Yan matan sun yi korafin rashin samun kudaden da aka samu ta hanyar gudunmawa.

'An mayar da su saniyar tatsa'

Misis Demm ta ce, "Ni a ganina, ana shafa wa tallafin da ake masu kashin kaji, kuma sai ya kasance ana yi wawure tallafin sai kawai a rika ba su wayoyin iPhone da iPad da kuma 'yan daloli nan da can kawai.''

Kwararriyar ta cigaba da jaddada damuwarta a kan 'yan matan, abin da ya kai ga wata hadaka tsakanin wata kungiya mai zaman kanta mai suna Murtala Muhammad Foundation, da Ma'aikatar Harkokin Mata a Najeriya, da kuma Ofishin jakadancin Najeriya da ke Amurka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sauran 'yan matan Chibok da ke karatu a jami'ar Amurka da ke jihar Adamawa, sun samu an killacesu daga idon jama'a

A watan Mayun shekarar 2016, aka cire bakwai daga cikin 'yan matan daga karkashin kulawar kungiyar agajin Najeriyar da ta kai su Amurka.

Bayan wata ganawa da iyayen 'yan matan Chibok din a Maiduguri, Ministar harkokin mata ta Najeriyar, Aisha Alhassan ta shaida wa manema labarai cewa, "Ana amfani da 'yan matan ne kawai domin samun kudade."

Paul Ali, mahaifin daya daga cikin 'yan matan, shi ma ya bayyana irin damuwarsa yana cewa, "Bisa labaran da muke samu, ga alamu ba karatu suke yi ba a Amurka, kamar yadda muka yi za to."

Ya kara da cewa, "Yanzu mun gane cewa ana amfani da 'ya'yanmu ne wajen neman kudi, kuma ba haka muka so wa 'ya'yanmu ba."

Emmanuel Ogebe, shugaban kungiyar bayar da agaji ta Education Must Continue Initiative, wanda ya dauki nauyin wasu daga cikin 'yan matan zuwa Amurka har shekara biyu, ya musanta zargin da ake, yana mai cewa suna samun ilimi da kulawa sosai.

Ya ce, "Na ziyarci iyayen 'yan matan Chibok din a arewa maso gabashin Najeriya, har ma da Mista Paul Ali, kuma na nuna masa hoton diyarsa a makaranta, da kuma hotunan wasu ayyuka da take yi a makaranta." In ji Mista Emmanuel.

Amma kuma Misis Demm ta nanata bukatar a killace 'yan matan, domin hakan ne kawai take ganin zai fi zamar wa 'yan matan alheri ga lafiyarsu.

Ta kara da cewa, ya kamata su gane abin da ya faru da su ne, sannan su dangana domin su iya gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata.

Asalin hoton, Fatima Akilu

Bayanan hoto,

Dokta Fatima Akilu, jagorar wani shirin kare al'umma daga tsangwama da wariya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar a baya

Manya da 'yan matan da 'yan mata da Boko Haram suka sace na fuskantar tsangwama da wariya bayan an kubutar da su, daga al'ummarsu, saboda wata al'ada ta tsanar wadanda aka yi lalata da su, ko fyade.

Dokta Fatima Akilu, wadda kwararriya ce kan tunanin dan adam, a baya ta jagoranci wani shirin kare al'umma daga tsangwama da wariya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar ta ce, "Bani da wata damuwa ga 'yan matan Chibok, saboda suna zagaye da masu ba su taimako, kazalika 'yan garin Chibok din suna sane da abin da ya faru, don haka ba za su fuskanci wariya ba."

Amma kuma ta kara da cewa, ''yawancin 'yan matan da aka sace ba sa samun irin wannan taimakon.''

Ta kuma kara da cewa, "Muna da dubban 'yan matan da aka sace da ba su ma kai shekarun 'yan matan makarantar Chibok din ba, wasu ma sun fi su dadewa a hannun 'yan Boko Haram, suna kuma dawowa cikin al'ummarsu ana musu korar kare saboda alakarsu da Boko Haram."

Akwai kuma fargabar cewa an sanya masu akidar 'yan ta'addan, saboda yawan amfani da mata wajen kunar bakin wake da kungiyar ke yi.

Dokta Fatima ta ce, "Wasunsu na dawowa da ciki ko da goyo, kuma ana nuna wa 'ya'yan da suka zo da su kiyayya matuka."

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaran da 'yan matan ke dawowa da su na fuskantar wariya da matukar kiyayya ne saboda ana musu kallon mugun iri da ke da alaka ta jini da Boko Haram.

Asalin hoton, ADAOBI TRICIA NWAUBANI

Bayanan hoto,

Zama a Najeriya sannu a hankali ba zai zo da wani kalubale ba ga 'yan matan, idan aka kwatanta da mugun yanayin da suka shiga, in ji Adaobi Tricia Nwaubani

An dai samar wa wata tawagar 'yan matan da suka kubuta daga hannun kungiyar damar karatu a jami'ar Amurka da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Akwai yiwuwar 'yan matan Chibok din 21 da aka sako kwanan nan bayan fiye da shekara biyu a hannun mayakan, ba za su shiga walwala a Amurka ba, har ma su manta da abin da ya faru dasu, kuma su cigaba da karatunsu, ba wai a mayar da su abin talla ga manema labarai ba.

Zama dai a Najeriya dai sannu a hankali ba zai zo da wani kalubale ba ga 'yan matan, idan aka kwatanta da mugun yanayin da suke shiga idan aka bayyana su a bainar jama'a.