Amurka: Ba ruwan gwamnati da batun Clinton da FBI

'Yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hillary Clinton ta musanta aikata ba daidai ba

Gwamnatin Amurka ta ce ba za ta ce uffan kan shawarar da hukumar bincike ta FBI ta yanke na bayyana aniyarta ta sake gudanar da bincike kan sakwannin email din Hillary Clinton ba.

Wani mai magana da yawun Shugaba Obama ya ce bai yadda cewa daraktan FBI, James Comey, na kokarin yin katsalandan ne a zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar Talata ta sama ba.

A makon jiya hukumar FBI ta ce ta gano wasu sabbin sakwannin emails da ka iya zama na Misis Clinton, kuma ta ce za ta bincika ko sun kunshi bayanan sirri.

A baya dai FBI ta soki 'yar takarar ta Democrat kan amfani da email din kashin kanta, lokacin da take sakatariyar harkokin waje.

Sai dai kuma ta wanke ta daga aikata wani babban laifi.

A wani taron siyasa a jihar Michigan, abokin hamayyarta Donald Trump na Republican, ya ce yana tunanin FBI ta samo "dimbin" sakwannin emails din Misis Clinton.

Ya kuma kara da cewa yana fata yanzu za a gano sakwannin da suka kai kimanin 33,000 da ya ke zargin an goge.