Ma'aikatar Lafiyar Kenya ta musanta Almundahana

Kasar Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'aikatar lafiyar ta ce ba a karkatar da kudin gwamnati ba, akasin rahotannin da wata jaridar kasar ta wallafa

Ma'aikatar lafiyar Kenya ta fito ta musanta zargin da aka yi mata na karkatar da wasu kudade kimanin dala miliyan 50.

Hakan na zuwa ne bayan da wata jaridar kasar, ta wallafa wani rahoto da ke dauke da binciken da ake gudanarwa kan zargin almundahana da aka yi da wasu kudade da aka ware, domin shirin samar da kulawa ga masu juna biyu kyauta.

Ma'aikatar lafiyar ta ce ba a karkatar da kudin gwamnati ba, akasin rahoton da wata jaridar kasar ta wallafa.

A wata sanarwa da Ma'aikatar ta fitar, ta ce jaridar da ke zaman kanta ta wallafa labarin nata ne ba tareda bari an kammala binciken ba, wanda hakan ya yaudari al'umma har ya kai ga ana tsammanin gwamnati ta rasa kusan dala miliyan 50.

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce tsakanin shugabannin jam'iyyun adawa, wadanda suka yi ta kira da a sallami duk jami'in da aka samu da hannu a ciki.