Mark Carney zai ci gaba da zama gwamnan bankin Ingila har 2019

Sanarwar Mr Carney ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa game da makomarsa
Bayanan hoto,

Sanarwar Mr Carney ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa game da makomarsa

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta yi maraba da matakin da gwamnan bankin Ingila ya dauka na cigaba da kasancewa a aiki na tsawon shekara guda.

Mark Carney ya ce zai cigaba da zama a ofishinsa har zuwa Yunin shekarar 2019 domin ya taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Birtaniya a lokacin da ta ke tattaunawa da tarayyar turai bayan 'yan kasar sun jefa kuri'ar neman kasar ta fice daga kungiyar.

Wannan sanarwa ta sa ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa game da makomarsa.

Mr Carney dai na samun suka daga 'yan siyasar da ke goyon bayan kasar ta fice daga tarayyar turai, saboda gargadin da ya rinka yi na cewa akwai yiwuwar samun koma baya a bangaren tattalin arziki idan har Birtaniya ta fice daga tarayyar turan.