Argentina: Cristina Fernandez ta gurfana a kotu

Ms Fernandez na daga cikin mutane 17 da aka yi sammacinsu

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ms Fernandez na daga cikin mutane 17 da aka yi sammacinsu

Tsohuwar shugabar kasar Argentina Cristina Fernandez de Kirchner ta gurfana gaban kuliya inda ake zarginta da aikata almundahana.

Ana dai zargin gwamnatinta da bayar da kwangila ga wani dan kasuwa Lazaro Baez wanda makusanci ne ga iyalanta.

Masu shigar da kara na zargin cewa yana saka wa Ms Fernandez ne ta hanyar biyan kudin dakuna a otel mallakin iyalan Kirchner.

Ita ce dai ta farko a cikin mutane goma sha bakwai da aka yi sammacinsu da za ta bayar da shaida akan zargin da ake mata.

Da take jawabi a wajen kotun, Ms Fernandez ta ce bita da kulli wanda ya gaje ta ya shirya mata.