Nigeria: Satar mutane 'na kara kamari'

Kwamishinan 'yansanda Ibrahim Idris
Bayanan hoto,

Jama'a sun ce ana matukar neman dauki daga hukumomin tsaro

Wani dan majalisar wakilan Najeriya ya ce matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa a wasu jihohin kasar ta yi kamari fiye da yadda kowa ke tsammani.

Hon. Abdulmalik Zubairu daga jihar Zamfara - daya daga cikin jihohin da ke fama da wannan matsalar- ya ce a mazabar da yake wakilta kadai an sace mutane kusan bakwai a cikin makonni biyu kawai.

Ya ce yanzu masu garkuwa da mutanen kan bi mutane har gidaje ko gonakkinsu su sace su.

Shi ma da yake zantawa da BBC bayan yin gyara da dokar hukunta masu satar mutane domin ta hada da hukuncin kisa, Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kano Honourable Kabiru Alhassan ya ce ko a kudancin jihar ma ana bin mutane har gona ana garkuwa da su.

Wakilin BBC a jihar ta Kano ya ce wannan matsalar na sa har mazauna wannan yankin na kauracewa gidajensu.