Ana gagarumin aikin ceton mahaka ma'adinai a China

Mahakar Shandong

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Hadurran ruftawar wuraren hakar ma'adinai na yawan faruwa a China duk da kokarin inganta matakan kariya.

An kaddamar wani da gagarumin aikin ceto wasu ma'aikatan hakar kwal 24 da mahaka ta rufta da su a kudu maso yammacin China, bayan fashewar wani abu.

Kafafen watsa labaran yankin sun ce fiye da ma'aikata 400 ne suka shiga aikin ceto mahaka ma'adinan da suka makale.

Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar 13 daga cikinsu wasu kuma 20 ba a san inda suke ba yayin da wasu mutane biyu suka kubuta da lami lafiya.

Lamarin ya faru ne ranar litinin a mahakar ma'adinai ta Jinshagou da ke lardin Chongqing a kudu maso yammacin kasar.

Mataimakin magajin garin birnin Chongqing inda lamarin ya faru, Ma huaping, ya ce har yanzu akwai fatan samun wadanda ake nema da rai.