Theresa Kachindamoto ta raba aure 840
Theresa Kachindamoto ta raba aure 840
Theresa Kachindamoto babbar jami'a ce ta gundumar Dedza, a tsakiyar Malawi, ta kuma yi amfani da karfin ikonta wajen taimakawa mata da 'yanmata.
A yankunan karkara na kasar Malawi, wasu iyaye na aurar da 'yayansu mata da ba su wuce shekara 12 ba.
Babbar jami'ar ta umarci jami'an da ke karkashinta su rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen auren wuri.
Ta kuma ja hankulan shugabannin al'umma da su dakatar da auren wuri.