MDD ta kori kwamandan soji a Sudan Ta Kudu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya kori kwamandan rundunar sojin Majalisar da ke Sudan ta Kudu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya kori kwamandan rundunar sojin Majalisar da ke Sudan ta Kudu, bayan wani bincike ya gano cewa dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar sun gaza kare fararen hula.

Binciken ya fito da zargin ma'aikatan agaji suka yi tunda farko na cewa, dakarun Majalisar Dinkin Duniya ba su ce komai ba lokacin da sojojin gwamnati suka kai hari wajen da ma'aikatan agaji na kasashen waje ke zaune, a yayin fadan bangarorin da aka yi a watan Yulin da ya wuce, a Juba, babban birnin kasar.

An kashe wani dan jaridar Sudan ta Kudu a harin, inda kuma aka lakada wa wasu ma'aikatan agaji duka tare da yi masu fyade.

Akwai rahotannin da ke cewa sojojin kiyaye zaman lafiyar, wadanda aka girke kilomita daya daga wajen da lamarin ya afku, sun gaza wajen gudanar da ayyukansu, kuma sun nuna halin ko-in-kula ga lamuran tsaro.