Dakarun Iraqi na luguden wuta a cikin birnin Mosul

Dakarun Iraqi a fagen daga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Iraqi na son karbe baki daya yankunan kasar da 'yan IS ke iko da su

Dakarun gwamnatin Iraqi da suka kutsa cikin birnin Mosul, da a karon farko tun bayan kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS sun karbe shi shekaru biyu da suka gabata, sun ce za su ci gaba da dannawa cikin birnin har sai baki dayansa ya dawo karkashin ikon gwamnati.

Mai magana da yawun sojojin Iaraqin Sabah al-Numan, ya shaidawa BBC cewa a yanzu dakarun su a shirye suke tsaf dan fara yaakin ta hanyar binciken kowannen gida.

Al-Numan ya kara da cewa duk da bata kashin da aka yi a jiya talata, wanda har aka yi nasarar kwato gidan talabijin da ke yammacin birnin Mosul da 'yan IS suka karbe iko da shi, dakarun su kalau suke ba tare da jin ko rauni ba.

Wakilin BBC da ke cikin tawagar su ya ce babu alamar sassauta ruwan bama-baman da sojiji ke yi, a daidai lokacin da suke kara dannawa dan fatattakar 'yan tawaye daga cikinsa.

Sai dai a nata bangaren MDD ta nuna damuwa kan makomar sama da fararen hula miliyan daya da ke suka makale a cikin birnin.